Hadisai daga Imam ALI (AS)

Hadisai daga Imam Ali (as)

Hadisai daga Imam Ali (as)


1-Imam Ali[AS] ya ce, “ Duk wanda ya gyara tsakaninsa da Allah to Allah zai gyara tsakaninsa da mutane,duk wanda ya gyara al’amarin lahirarsa to Allah zai gyara al’amarin duniyarsa.” 2- Imam Ali[AS] ya ce, “ Ya kai ]an Adam idan ka ga Allah Ta’ala yana yi maka ni’imomi alhali kana saba masa to ka yi hankali.” Wato zai kasance kenan istidraji ga mutum. 3- Imam Ali[AS] ya ce, “ Idan ka samu iko kan ma}iyinka ka yi afuwa gareshi a matsayin godiya ga Allah kan wannan iko da ka samu akansa. 4-Imam Ali[AS] ya ce, “Mutane basu bar wani abu ba na al’amarin Addininsu saboda mas’lahar duniyarsu face Allah Ta’ala ya bude masu abunda ya fi haka tsanani.” 5- Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda yasa kansa a in da za a iya tuhumarsa,to ka da ya zargi duk wanda ya munana masa zato.”misali mutum yaje in da ba a tsamanin samun ma’abucin addini ko mutumin kirki a wajen. 6-Imam Ali[AS] ya ce, “Mafificin ayyuka sune wa]anda ka tilasta kanka wajen aikatasu.” Wato ayyukan da mutum yayi mujahada wajen aikatasu,ayyukan na ibada ne ko umarni ko hani. 7-Imam Ali[AS] ya ce, “Ina mamakin wanda yake cire tsamanni daga rahamar Allah Ta’ala alhali ga istigfari.” 8-Imam Ai[AS] ya ce, “Allah Ta’ala yana da ha}}i ga kowace ni’ima da yayi ma mutum,wanda ya bada hakkin sai Allah ya kara masa,wanda kuma bai bayar ba to akwai yiyuwar ni’imar ta gushe.”Hakkin ko wace ni’ima da Allah yayi ma mutum shine godiya ga Allah kanta,ya kuma kasance ka da mutum yayi amfani da ni’imar da Allah yayi masa wajen saba masa. 9-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda aikinsa ya maida shi baya to nasabarsa ba zata kaishi gaba ba.”Wato idan mutum bai yi kyakkyawan aiki ba a wannan gida na duniya to ranar lahira nasabarsa ba zata amfane shi ba.” 10-Imam Ali[AS] ya ce, “Kuji tsoron asa ma Allah a boye domin mai ganin boyen shine zai yi hukunci ranar kiyama.”

Comments

Popular posts from this blog

Introduce myself